Tarihin mazan jiya

Tarihin mazan jiya Advertising

05/01/2026
SANARWA KAN MATAKIN GAGGAWAR TSARO A FAƘAƘA DA ƘARIN DAUKAR JAMI’AN SOJOJI DA ‘YAN SANDA’Yan Najeriya,A yau, ganin yadda...
27/11/2025

SANARWA KAN MATAKIN GAGGAWAR TSARO A FAƘAƘA DA ƘARIN DAUKAR JAMI’AN SOJOJI DA ‘YAN SANDA

’Yan Najeriya,

A yau, ganin yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa, na yanke shawarar ayyana dokar ta-baci a sashin tsaro kuma na bayar da umarnin daukar karin jami’an tsaro cikin Sojoji da ‘Yan Sanda.

Da wannan sanarwa, an ba wa soja da ‘yan sanda damar daukar karin ma’aikata. Rundunar ‘yan sanda za ta dauki karin jami’ai 20,000, wanda zai kai adadin zuwa 50,000.

Ko da yake na riga na amince da sabunta cibiyoyin horas da ‘yan sanda a fadin kasa, wannan sanarwa ta ba su damar amfani da sansanonin NYSC a matsayin wuraren horaswa.

Jami’an da za a cire daga aikin gadin manyan mutane (VIP) za su sami horaswar gaggawa domin su koma aiki a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.

Hukumar DSS ma ta samu izinina ta tura jami’anta cikin dazuka domin kawar da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga. Haka kuma na ba su umurnin daukar karin jami’ai domin tsaro a dazuka. Ba za a sake samun wurin boyewa ga miyagu ba.

’Yan Najeriya, wannan gaggawa ce ta kasa, kuma muna mayar da martani ta hanyar tura karin jami’an tsaro musamman a yankunan da matsalar tsaro ta fi tsanani. Wannan lokaci ne da kowa zai sa hannu. Mu tashi mu taimaka wajen ceto kasarmu.

Ina yaba wa jami’an tsaro bisa kokarinsu har aka kubutar da ɗalibai 24 na Kebbi da masu ibada 38 da aka sace a Jihar Kwara. Za mu ci gaba da yin iyakar kokari domin ceto sauran daliban makarantar Katolika da har yanzu ake garkuwa da su a Jihar Niger.

Ga jagoranci da jami’an Sojojinmu, ina yaba da jarumtar ku da sadaukarwarku. Wannan lokaci ne mai wahala ga kasa da ga rundunar soji. Ina umartar ku da ku kasance masu kishi, ku dawo da zaman lafiya, kuma ku tsaya tsayin daka wajen kiyaye ka’idoji da gaskiya. Kada a yarda da sakaci ko hada baki ko rashin bin doka. Mutanen Najeriya suna dogaro da ku, kuma gwamnati za ta ba ku duk goyon bayan da kuke bukata.

Bugu da kari, gwamnatimmu za ta tallafa wa jihohin da s**a kafa rundunonin tsaro domin kare jama’arsu daga barazanar ‘yan ta’adda da suke kokarin lalata zaman lafiya
Ina kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta fara duba dokokinmu domin ba wa jihohin da ke bukata damar kafa rundunar ‘yan sandar jiha.

Jihohi su sake tunani game da kafa makarantu masu zaman board a yankuna masu nisa ba tare da tsaro mai inganci ba. Masallatai da coci-coci su rika neman kariyar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a duk lokacin da suke taron ibada, musamman a wuraren da ake ganin haɗari.

Gwamnatinmu ta kirkiro Ma’aikatar Kiwo domin magance rikice-rikicen manoma da makiyaya. Ina kira ga dukkan kungiyoyin makiyaya su amfana da wannan damar, su daina kiwo a fili, su mika makamai bisa ka’ida. Kiwo na zamani shi ne mafita domin dorewar kiwo da zaman lafiya a kasa. Gwamnatin Tarayya tare da jihohi za su yi aiki tare domin magance wannan matsala gaba ɗaya.

Ina jajanta wa iyalan da s**a rasa ‘yan uwansu a hare-haren da s**a faru a Kebbi, Borno, Zamfara, Niger, Yobe da Kwara. Haka kuma ina tuna jarumai sojojinmu da s**a yi shahada, ciki har da Brigadier-General Musa Uba.

Ga masu tunanin suna iya gwada juriyarmu, kada su dauki nutsuwa a matsayin rauni. Wannan gwamnati tana da ƙarfin hali da azamar kare kasar nan da tabbatar da zaman lafiya ga ‘yan kasa.

Ina kuma jajanta wa iyalan wadanda s**a rasa rayukan ‘yan uwansu a hare-haren baya-bayan nan a Kebbi, Borno, Zamfara, Niger, Yobe da Kwara. Ina kuma karrama jarumai sojojinmu da s**a bayar da rayukansu, ciki har da Brigadier-General Musa Uba.

’Yan uwana ‘yan Najeriya, ina rokonku kada ku bari tsoro ko damuwa su rinjaye ku. Mu tashi tsaye a dunkule wajen kare ‘yancinmu da kimarmu. Gwamnatinmu za ta ci gaba da tabbatar da zaman tare cikin kwanciyar hankali da kare hadin kanmu. Ina kira ga dukkan ‘yan Najeriya su kwantar da hankali, su kasance masu lura da abin da ke faruwa. A rika kai rahoton duk abin da ake zargin yana da hatsari. Ku yi aiki tare da jami’an tsaro. Muna wannan fada tare, kuma tare zamu yi nasara.

Allah ya ci gaba da albarkar Najeriya ya kuma kare sojojinmu.

PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU, GCFR
A*O ROCK VILLA
NOVEMBER 26, 2025

YANZU-YANZU: Ga Wata Babbar Damar Dogaro Da Kai Ga Matasa Daga Gwamnatin TarayyaIna matasan Najeriya! Gwamnatin Shugaba ...
28/10/2024

YANZU-YANZU: Ga Wata Babbar Damar Dogaro Da Kai Ga Matasa Daga Gwamnatin Tarayya

Ina matasan Najeriya! Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da sabon Shirin ta mai taken “Renewed Hope Employment Initiative”. Wannan shirin zai samar da aikin yi da koyar da sana’o’i ga matasa 93,731 a faɗin Najeriya. Bugu da ƙari, zai bada jari na fara sana’o’in ga waɗanda s**a samu horon, sannan kuma za a baiwa wasu damar samun lamuni dan gudanar da ƙananu da matsakaitan kasuwanci.

Shirin na daga matakin da Gwamnatin ke ɗauka don wadata ƴan Najeriya da aikin yi, ƙarfafa dogaro da kai da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.

Masu buƙata zasu iya shiga adreshin yanar gizo ta intanet kamar haka;

www.nde.gov.ng

Abubuwan da ake buƙata domin yin rejista; Asusun Email, hoton fasfo, nambar shedar ɗan ƙasa NIN.

Za a tuntubi waɗanda aka zaba kai tsaye ta kan adreshin Email din da s**ai rejista da shi. Sannan kuma akwai alawus da za a baiwa dukkan waɗanda za a baiwa horon a faɗin ƙasar nan.

An fara rejista a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2023, za kuma a rufe a ranar Talata 31 ga watan Disamba, 2024.

Kada ku bari ayi babu ku.

Wani Ya Saki Matarsa Sabo Taje Taron Jam'iyyar APC.An sake samun wani sabon takardar saki, tsakanin Lawal Abdulkadir, da...
13/10/2024

Wani Ya Saki Matarsa Sabo Taje Taron Jam'iyyar APC.

An sake samun wani sabon takardar saki, tsakanin Lawal Abdulkadir, da matar sa Zainab Ismail Tofa wacce akafi sani da Ummi sakamakon taje taron APC.

BIN DIDDIGI: Shin Da Akwai Luwąɗi, Mąɗígò Da Sauyin Jiɲsi A Cikin Yarjejeniyar Samoa Da Nąjeriya Ta Sa Hannu?Binciken PR...
08/07/2024

BIN DIDDIGI: Shin Da Akwai Luwąɗi, Mąɗígò Da Sauyin Jiɲsi A Cikin Yarjejeniyar Samoa Da Nąjeriya Ta Sa Hannu?

Binciken PREMIUM TIMES ya gano cewa akwai batun luwáɗi, maɗígo da sauyin jinsi a daftarin farko na Yarjejeniyar Samoa amma rashin amincewar wasu daga cikin ƙasashe ya tilastawa Tarayyar Turai, EU ta cire sassan daga cikin daftarin.

A ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito yadda wasu daga cikin ƙungiyoyin addini da na ci gaban al’umma a cikin ƙasar nan ke nuna damuwa game da wasu sassa a cikin yarjejeniyar $150 biliyan ta Samoa wacce gwamnatin Najeriya ta sa hannu a ranar 28 ga Yuni waɗanda s**a sharɗanta kare haƙƙin ƴan luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi.

Rahoton jaridar ya dogara ne da ra’ayin da wani lauya mazaunin Lagos, Sonnie Ekwowusi ya rubuta, kuma jaridun BusinessDay, Vanguard da TheCable s**a wallafa.

Rahotannin sun jawo masu sharhi sun yi caa kan gwamnatin tarayya inda suke s**arta da yin watsi da mutunci da tabiyyar ƴan Nigeria saboda kwaɗayin bashin ƙasashen waje.

Sai dai, gwamnatin tarayya, a wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’uma Mohamed Idris ya fitar da yammacin Alhamis, ta ce ba ta sa hannu akan yarjejeniyar ba “sai bayan nazari da tattaunawa tsakanin jami’an ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, ma’aikatar hulɗa da ƙasashen waje da kuma ma’aikatar shari’a.”

Mohammed Idris ya ƙara da cewa gwamnati ta tabbatar “Babu wani daga cikin sassan yarjejeniyar 103 da ya saɓawa Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 da sauran dokokin Nigeria.”
Gwamnatin Nigeria ta sa hannu a kan yarjejeniyar ne watanni bakwai bayan da aka fara sa hannu akanta a Samoa.

Gwamnatin ta ce ta jinkirta amincewa da ita ne domin samun damar tantance dokar dalla-dalla saboda tabbatar da cewa babu wani sashi da ya saɓawa dokokin Nigeria.

A bara ne dai kakakin Ma’aikatar Hulɗa da Ƙasashen Waje Francisa Omay ta bayyanawa manema labarai cewa “Muna sanar da al’umma Nigeria ba ta cikin ƙasashen da s**a sa hannu a Yarjeniyar Samoa ranar Laraba 15 ga Nuwamba 2023 saboda ba ta kai ga amince wa da dokar ba.”
Ta kuma ce “A yanzu haka masu ruwa da tsaki na Nigeria na ci gaba da nazarin yarjejeniyar domin tabbatar da cewa ba ta saɓa wa dokokin ƙasar nan ba.”

PREMIUM TIMES ta ga saƙon da gwamnatin Nigeria ta aikewa EU a lokacin, inda ta ƙalubalanci 13 daga cikin sassan yarjejeniyar.

Daga ciki, gwamnatin Nigeria ta ƙalubalanci Sashi na 9.2, wanda ya shafi Haƙƙin bil’Adama, dimokraɗiyya da aiwatar da doka inda ta ce dama Tsarin Mulkin Nigeria ya na da tanadi game da haƙƙin bil’Adama.

Wannan ya haɗa da “haramcin nuna wariya ta kowacce irin fuska, da ya bai wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa damar yin kowacce irin doka da ta kare haƙƙoƙin dukkan rukunin ƴan ƙasa da s**a shafi siyasa, tattalin arziki, da ilimi. Wannan ya dace da tanade-tanaden Majalisar Ɗinkin Duniya kan Kare Haƙƙi wadda tuni Nigeria ta sa hannu.”

Wasu sassan da gwamnatin Nigeria ta ƙalubalanta sun haɗa da Sashi na 1 (Manufofi), Sashi na 3 (Tattaunawa kan haɗin kai), Sashi na 4 (Daidaituwar Manufa), da Sashi na 79 (Haɗin kai kan ƙungiyoyin ƙasashen duniya da Majalisu).

Bugu da ƙari, gwamnatin ta ƙalubalanci Sashi na 19 (Manyan laifuffuka da s**a shafi ƙasashen duniya); Sashi na 36 (Daidaiton jinsi da kyautata rayuwar mata da ƙananan yara); Sashi na 49 (Cinikayya da cigaba mai ɗorewa); Sashi na 51 (cinikayyar ayyukan fasaha) da Sashi na 97 (Sauran yarjeniyoyi da shirye-shirye).

Akwai kuma Sashi na 101 (Sasanta saɓani da sauke nauyi), Sashi na 22 (Ayyukan fasah), Sashi na 40 (Daidaita jinsi da inganta rayuwar mata), Sashi na 51 (Sauyin yanayi), da Sashi na 3 (Canjin kuɗi).

Tantance zargin
PREMIUM TIMES ta yi nazarin yarjejeniyar mai shafi 172 domin tantance ko akwai batun luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi kamar yadda Daily Trust da sauran jaridu s**a wallafa.

Mr Ekwowusi, wanda shi ne ya rubuta maƙalar da jaridun s**a dogara da ita wurin wallafa rahotanninsu, ya yi zargin cewa wasu sassan yarjejeniyar sun halatta luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi ta bayan gida.

Lauyan, wanda shi ne shugaban Kwamitin kula da Haƙƙoƙin Bil’Adama da Tsarin Mulki na Ƙuniyar Lauyoyi ta Afirka (AfBA), ya rubuta a maƙalarsa da Daily Trust ta wallafa ranar 3 ga Yuli cewa “Wasu daga cikin sassan yarjejeniyar, musamman ma Sashi na 2.5 da Sashi na 29.5 sun halatta maɗigo da sauyin jinsi, zubar da ciki, keta zarafin matasa, da sauran ɗabi’u da s**a saɓawa al’adun ƙasashen Afirka.”

Sai dai wannan fassarar ta Mr Ekwowusi ta saɓa da abinda wakilinmu ya gano a cikin kundin yarjejeniyar da ya nazarta.
Sashe na 2.5 na yarjejeniyar ya ce “Ƙasashen zasu ɗauki matakan kula da yi wa jinsina adalci tare da tabbatar da cewa an yi la’akari da jinsi a duk wasu dokokin gwamnati,” wato bai kawo wata maganar jima’i ba kamar yadda Mr Ekwowusi ya yi iƙirari.
Haka kuma lauyan ya yi kuskure wurin fassara sashi na 29.5 wanda ya ce: “Ƙasashen za su tabbatar da kowa ya samu kayan kula da lafiyar da ta shafi jima’i da haihuwa ciki har da tsarin iyali, ilmintarwa da faɗakarwa, da kuma shigar da lafiyar masu haihuwa cikin tsare-tsare da manufofin ci gaban al’umma.”

Saɓanin da’awar lauyan, wacce jaridun s**a yayata babu wani wuri da aka yi batun luwaɗi da maɗigo a wannan sashen.

Daftarin da muka yi nazari da kuma sanarwar da Tarayyar Turai s**a fitar sun bayyana cewa Yarjejeniyar Samoa ta mai da hankali ne wurin warware ƙalubalen da suke addabar duniya.

Manfufofinta na son bada gudunmawa ne wurin cimma manufofin ci gaba mai ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Yarjejeniyar Paris da aka amince da ita ƙarƙashin Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi.
A ɗaya daga cikin sanarwar da ta fitar, EU ta ce abubuwan da yarjejeniyar ta fi bai wa muhimmanci sun haɗa da kare haƙƙin bil’Adama, dimokraɗiyya da ingantaccen shugabanci, zaman lafiya da tsaro, ci gaban al’umma, bunƙasar tattalin arziki wacce take taɓa kowa, kula da muhalli da sauyin yanayi, da kuma hijirar al’umma.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an yi ta sa-toka-sa-katsi daga daftarin farko zuwa samar da kundin ƙarshe na yarjejeniyar – sanarwar gwamnatin tarayya ta bara da wata sanarwa ta Tarayyar Turai sun tabbatar da hakan.

Sanarwar ta EU ta ce yarjejeniyar za ta bunƙasa, kare, da tabbatar da haƙƙoƙin bil’Adama, waɗanda s**a shafi zamantakewa, siyasa, tattalin arziki, da al’ada sai dai “wasu daga cikin ƙasashen Afirka, Carribean da Pacific sun ƙi amincewa da batun maɗigo da sauyin jinsi – abinda har cikin ƙasashen EU ba duka ne s**a amince da shi ba.”

A sanarwar, EU ta yi batun tanadin Sashi na 36.2 in da ta ce: “an daidaita cewa, ƙasashen za su tabbatar da aiwatar da dukkan yarjeniyoyin ƙasashen duniya da s**a riga s**a sa musu hannu – musamman Taron Rage Yawan Al’umma, matakan kare haƙƙoƙin jima’i da haihuwa da Matsayar Beijing kan daidaiton jinsi da sauran yarjejeniyoyin da s**a biyo baya.”

Sai dai, sanarwar ta ce wannan yarjejeniyar “ba ta cimma manufofin masu tattaunawar EU ba.”
PREMIUM TIMES ta fahimci cewa da fari an sa sassan da s**a yi magana kan halatta luwaɗi da maɗigo cikin Yarjejeniyar Samoa, amma rashin amincewar ƙasashen ta tilastawa EU cire waɗannan sassan daga kundin na ƙarshe.

Wannan ya ƙara fitowa fili idan aka yi la’akari da wata sanarwar ta EU, inda ta ce ta na maraba da amincewar da ƙasashen s**a yi na bunƙasa haƙƙoƙin bil’Adama ba tare da kowacce irin wariya ba “sai dai ta na takacin cewa Yarjejeniyar ta gaza wurin fitowa ɓaro-ɓaro ta haramta wariya kan bambancin tsarin jima’i da sauyin jinsi.”

EU ta kuma roƙi ƙasashen su “guji nuna bambanci game da tsarin jima’i tare da kawo ƙarshen hukuntawa tare da hukuncin kisa ga mutanen da suke maɗigo da sauyin jinsi...”
Kammalawa
Ta tabbata cewa EU ta amince da luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi kuma ta yi ƙoƙarin jawo ƙasashen dake cikin Yarjejeniyar Samoa su bai wa ƴan luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi kariya. Sai dai ƙin amincewar wasu daga cikin ƙasashen, ciki har da Nigeria ya tilasta mata cire wannan sashin daga cikin kundin da ta wallafa a shafinta ranar 22 ga Disamba 2023.
Lokacin da aka wallafa kundin, Nigeria ba ta kai ga sa hannu kan yarjejeniyar ba, wacce EU ta ce ta fara aiki daga bana kuma za ta ƙare aikinta nan da nan da shekaru 20.

A yanzu haka dai, Sashi na 101 na sabuwar yarjejeniyar ya mayar da hankali ne kan sasanta rikici da sauke nauyi.

Saɓanin abinda aka yaɗa a wasu sassa na kafafen yaɗa labarai, Sashi na 2.2. na sabuwar yarjejeniyar ya bayyana cewa: “Ƙasashen sun jaddada ƙudirinsu na samar da kyakkyawar alaƙa tsakaninsu ta hanyar girmama alfarmar kowacce ƙasa, da kuma rashin yin amfani da barazana ko ƙarfi wurin keta iyaka ko ƴancin kan wata ƙasa ba, ko kuma kowacce irin hanya da ta saɓawa Kundin Tsarin Mulkin Majalisar Ɗinkin Duniya.”

Nigeria, a matsayinta na ƙasa mai cikakkiyar iko ta sa hannu kan dokar da ta haramta auratayya tsakanin jinsi guda a zamanin Shugaba Goodluck Jonathan.

Wannan ne ya sa masu sharhi ke ganin bai kamata Nigeria ta sa hannu a Yarjejeniyar Samoa ba.

Sai dai masana sun mayarwa da irin waɗannan martani, inda s**a ce irin wanann yarjejeniyar ta ƙasashen duniya, ko da an sa mata hannu, dole ne sai an tafka muhawara a Majalisar Dokoki ta Tarayya kamar yadda Sashe na 12(1) na Kundin Tsarin Mulkin Nigeria na 1999 ya tanada.

Rabiu Yusuf, shugaban Kwamitin kula da Yarjejeniyoyin Ƙasashen Duniya na Majalisar Wakilai da Asabe Ndahi, Jami’ar Tsare-tsare ta Cibiyar Kukah, sun bayyana cewa kawo yanzu ba a saka Majalisar Dokoki cikin sabgar Yarjejeniyar Samoa ba.

Mr Yusuf wanda ya yi jawabi a tattaunawar intanet da Cibiyar Kyautata aikin jarida ci gaban al’umma (CJID) ta shirya domin fahimtar matsayin Nigeria game da Yarjejeniyar Samoa ya ce kundin ya bayyana abubuwa da yawa da ƙasar nan za ta amfana da su.
Hukunci
Saɓanin abinda wasu sassa na kafafen yaɗa labarai s**a ruwaito, babu wani sashe da ya shafi luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi a cikin Yarjejeniyar Samoa wacce Nigeria ta sa hannu a kai, bisa binciken da PREMIUM TIMES ta yi.

Rahoton Daily Trust bai kawo wani sashe da ya wajabta kare haƙƙin masu luwaɗi, maɗigo da sauyin jinsi ba sai dai ruwaito ra’ayin Mr Ekwowusi, duk da cewa a cikin rahoton sun kawo hirarsu da sakataren gudanarwar NSCIA wande ya ce majalisar ba ta ga wani abu da ya shafi auren jinsi a cikin daftarin yarjejeniyar gwamnatin tarayya ta ba ta, ta duba kafin rattaba hannu.

Haka kuma, fassarar da Mr Ekwowusi, wannan lauyan mazaunin Lagos ya yi a ra’ayin da ya ɓatar da kafafen yaɗa labaran da s**a dogara da shi ba daidai ba ce.

BABBAR MAGANA: An garzaya da wani magidanci Asibiti bayan ya sha maganín maza, kayan aikinsa ta miƙe tsaye carr taƙi kwa...
10/05/2024

BABBAR MAGANA: An garzaya da wani magidanci Asibiti bayan ya sha maganín maza, kayan aikinsa ta miƙe tsaye carr taƙi kwanciya.

Kamar yadda kuke gani gata nan ta miƙe tsaye ko wándo ya gagara sakawa.

28/04/2024

Allah mun godema da kayi mu musulmai

🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔

Address

Rimin Dako Cikin Gari
Abuja
KKM

Opening Hours

Monday 06:00 - 05:00
Tuesday 06:00 - 05:00
Wednesday 06:00 - 05:00
Thursday 06:00 - 05:00
Friday 06:00 - 05:00
Saturday 06:00 - 05:00
Sunday 06:00 - 05:00

Telephone

+2348138683755

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tarihin mazan jiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Museum

Send a message to Tarihin mazan jiya:

Share

Category