11/09/2023
HARIN SEPTEMBER 11, 2001
A Rana Mai Kamar Ta Yau A ranar 11 ga watan Satumbar 2001, ‘yan ta’ad-da s**a kai wa Amurka hare-hare ta hanyar amfani da jiragen sama hudu, wadanda s**a yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a New York, Pennsylvania da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.
Ran 11 ga watan Satumban 2001 wasu ƴan ƙunar baƙin wake s**a ƙwace iko da jiragen dakon fasinjojin Amurka kuma s**a faɗa wasu dogayen gine-gine biyu a birnin New York kuma s**a kashe dubban mutane.Harin ya kasance ɗaya daga cikin hare-hare mafiya muni a wannan ƙarnin, ba ga Amurkawa ba kawai ga duniya baki ɗaya.
Wa aka so a kai wa hari?
Wasu ƙananan tawagogin mahara sun ƙwace iko da jirage huɗu da ke tafiya a sararin samaniyar gabashin Amurka. Daga nan sai s**a ja ragamar tuƙin jiragen s**a auka manyan gine-gine a New York da Washington. Jirage biyu sun faɗa cikin tagwayen ginin Twin Towers na Cibiyar Kasuwanci ta Duniya wato World Trade Centre a New York. Jirgin farko a ya fada North Tower wadda da ƙarfe 8:46 ko ƙarfe 13:46 agogon GMT. Na biyun kuma ya fada ɗaya ginin da ƙarfe 09:03. Gine-ginen sun k**a da wuta kuma mutane sun maƙale a ciki inda hayaƙi ya turniƙe gaba ɗaya birnin. Cikin ƙasa da sa'a biyu, tagwayen gine-ginen masu hawa 110 s**a rushe.
Da ƙarfe 09:37 jirgi na uku ya auka sashen yamma na ginin Pentagon - babbar hedikwatar ma'aikatar tsaron Amurka da ke wajen Washington DC, babban birnin Amurka. Jirgi na huɗu ya faɗi a wani fili a Pennsylvania da ƙarfe 10:03 bayan da fasinjojin s**a ƙalubalanci maharan. Ana tunanin maharan sun yi ƙoƙarin kai hari ne kan ginin majalisar dokoki na Capito; Building da ke Washington DC.
Mutane nawa ne s**a mutu?
Gaba ɗaya, mutum 2,977 (ban da maharan 19) s**a rasa rayukansu mafi yawansu a birnin New York. Duka fasinjojin 246 da ma'aikatan jiragen hudu sun rasu A tagwayen gine-ginen mutum 2,606 sun rasu - a take ko daga baya sanadin raunukansu.
A Pentagon, mutum 125 ne s**a rasu.