13/05/2026
DAULAR DAN FODIO JIYA DA YAU
FITOWA TA BIYU:
"HAUSAWA DA ASALIN SU, ASALIN KALMAR HAUSA,MAZAUNIN SU, AL'ADUN SU, ILIMIN SU.WASANNIN SU, SANA'O'IN SU, ADDININAN SU,"
ASALIN HAUSAWA:
HAUSAWA: wani jinsi ne na jama'a da s**a samu kansu mafi yawa a yammacin Afrika, mutane ne da s**a kafa garuruwa daban-daban, sannan duk garin da s**a kafa suna da jagoranci na sarautarsu.
Ba su samu damar haɗa kansu wuri guda ƙarƙashin tuta ɗaya ba, hakan ya sa ake kiran kowanne da sunan garinsu da kuma sunan sarautarsu.
Yana Daga Abin da ya zo A tarihi, ƙasar Hausa na da manyan garuruwa guda bakwai inda s**a fara zama A Wannan Yanki Namu Ana Kiran su da "HAUSA BAKWAI", waɗannan garuruwa sune kamar haka:
Daura
Gobir
Kano
Katsina
Zazzau
Rano
Birom.
Fitaccen masanin tarihin Hausawa, Farfesa Abdullahi Sa'id da ɗalibinsa kuma Farfesa Mahadi Adamu, sun bayyana cewa "Asalin Hausawa sun taho ne daga yankin Arewacin jamhuriyyar Nijar, wajen Agadas a yanzu, lokacin da Hamada ta fara tsanani sai neman waje mai danshi da lema da ruwa ya sa wasun su s**a fara sauya matsuguni" s**a rika komawa waɗancan garuruwa da aka lissafa a sama da ke Najeriya.
"Waɗanda s**a fara kafa tarihi a cikin Hausawa sune Daurawa da s**a bunkasa sai s**a janyo hankalin mutane da dama daga mabanbantan wurare ciki harda Larabawa", in ji farfesa Mahadi Adamu.
To masu salon Magana kan ce zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, ko da al'adunsu s**a fara cudanya sai kuma sabbin matsaloli s**a bijiro, da s**a haɗa da yunwa da kuma yake-yake, a nan ne wasunsu s**a fara hijira suna kafa wasu garuruwan da kuma sarautunsu, duk inda s**a kafa gari sai su naɗa sarautarsu, da dama suna alakanta sarautarsu da ta Daura, amma wasu ba su alakanta ba.
Farfesa Tijjani Muhammad Naniya ya ce "a wani kaulin kuma ana ganin Hausawa sun samo asali ne daga yankin gabashin Afrika, can wajen Habasha, dalili kuwa shi ne al'adun gargajiya irin na wannan wuri sun zama kusan daya da irin na Hausawa, domin kamar yadda Hausawa ke bautawa rana kafin zuwan musulunci haka su ma suke bauta wa rana, sannan kayan da suke sanyawa ma yafe ne kamar Hausawa, kana gidajensu ma na rufin bunu ne kamar yadda na Hausawa suke.
Sannan har yau har gobe akwai irin wadannan Hausawa a Habasha."
ASALIN KALMAR HAUSA DAGA MASANA DABAN DABAN:
Masana tarihi da harshe sun kawo ra’ayoyi mabamban ta game da asalin kalmar “Hausa”. Ga wasu daga cikin ra’ayoyin:
Ra’ayin Palmer
H. R. Palmer ya bayyana cewa: "kalmar Hausa ta samo asali ne daga kalmar “Habasha” ko “Habe”, wadda ake dangantawa da wasu mutane daga Gabas. Ya yi imanin cewa canjin lafazi ne ya mayar da ita “Hausa”.
Ra’ayin Barth
Heinrich Barth ya nuna cewa: "kalmar Hausa tsohuwar suna ce ta al’ummar da s**a zauna a yankin Sudan ta Yamma tun da dadewa, kuma Larabawa sun riƙa amfani da ita wajen kiran mutanen yankin".
Ra’ayin Smith
Abdullahi Smith ya bayyana cewa: "Hausawa Ba baƙin al’umma ba ne daga waje, don haka kalmar Hausa tana da alaƙa da mutanen cikin gida da harshensu tun asali".
Ra’ayin M. G. Smith:
M. G. Smith ya danganta kalmar Hausa da tsarin zamantakewa da siyasar ƙasar Hausa, yana ganin sunan ya samo asali ne daga haɗuwar al’umma masu harshe iri ɗaya.
Ra’ayin Bargery
George Percy Bargery ya nuna cewa kalmar Hausa ta daɗe tana wakiltar harshe da al’ada kafin zuwan Turawa, kuma tana nufin mutanen da ke magana da harshen Hausa.
Atakaice Da Babu Wani Jamhurin Malamai Ko Masana Tarihi Da S**a Hadu A magana Daya Kan Asalin Kalmar Hausa ko Hausawa Bari dai Kowa Yana Gina Maganar Sa Ne akan Ra'ayin sa
Allah ne Masani
AL'ADUN HAUSAWA, KASUWAN CI, ADDINI D.S:
Kasancewar Kabilar Hausa Kabila ce Mai Dogon Tarihi Da Wayewa Da Mu'amala da Wasu Kabilun Da Dama Hakan Yasa Suna da Al'adu Nasu Tun Kafin Zuwan Musulunci Hausawa Da Turawa. Waɗannan al’adu sun shafi rayuwa gaba ɗaya kamar aure, haihuwa, sana’a, sutura da zamantakewa.
1. Addini da Bautu
Hausawa sun kasance masu bautar iskoki da gumaka. Sun yi imani da:
Tsafi
Bori
Camfi
Bautar iskoki da bishiyoyi
Suna neman kariya ko waraka ta wurin boka da matsafa.
2. Sana’o’i
Hausawa sun kasance ƙwararru wajen sana’o’i kamar:
Noma
Kiwo
Jima
Rini
Saƙa
Ƙira
Fatauci
3. Aure
Auren Hausawa yana gudana ne bisa al’ada. Ana:
Neman aure ta hannun iyaye
Baiko
Sadaki
Bukukuwan aure da waƙoƙi
4. Sutura
Maza suna sanya:
Riga
Wando
Hula
Mata kuma suna sanya:
Zani
Riga
Gyale
Kayan ado na gargajiya
5. Abinci
Abincin Hausawa ya haɗa da:
Tuwo
Fura
Kunu
Dambu
Nama da madara
6. Mulki
Hausawa suna da tsarin sarauta tun da dadewa. Akwai:
Sarki
Hakimai
Masarauta
Majalisar dattawa
7. Wasanni da Nishaɗi
Suna yin:
Kokawa
Dambe
Kalangu
Waƙoƙin baka
Tatsuniya.
ILIMIN HAUSAWA :
Hausawa suna da irin nasu ilimin tun kafin zuwan Musulunci da Turawa. Wannan ilimi ya shafi yadda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
1. Ilimin Sana’a
Hausawa sun kware wajen koyon sana’o’i kamar:
Noma
Kiwo
Ƙira
Saƙa
Rini
Jima
Fatauci
Iyaye ne ke koya wa ’ya’yansu waɗannan sana’o’i tun suna yara.
2. Ilimin Magunguna
Hausawa sun san magungunan gargajiya daga:
Ganyaye
Saiwoyi
Itatuwa
Ƙasa da wasu abubuwan halitta
Suna amfani da su wajen warkar da cututtuka daban-daban.
3. Ilimin Taurari da Yanayi
Hausawa sun iya gane:
Lokacin damina
Lokacin fari
Yanayin noma
Ta hanyar kallon:
Taurari
Wata
Iska
Gizagizai
4. Ilimin Zamantakewa
Suna koyar da:
Ladabi
Biyayya
Girmama na gaba
Zumunci
Riƙon amana
Ana samun wannan ilimi ta tarbiyya da tatsuniyoyi.
5. Ilimin Mulki
Hausawa sun san yadda ake gudanar da mulki da shari’ar gargajiya ta hanyar:
Sarki
Hakimai
Masu unguwa
Majalisar dattawa.
6. Ilimin Adabi
Hausawa na da ilimin:
Tatsuniya
Karin magana
Waƙoƙin baka
Hikaya
Waɗannan suna koyar da hikima da darussa ga al’umma.
Atakai ce idan kayi duba na tsanaki zakaga cewa kabilar Hausa kabila ce wacce take da tsari irin nata,take da ilimi da wayewa ta mu'amala wanda ko da turawa s**azo sun sha wahala sabida sun same su da tsari na shugabanci da na addini da kuma na zamantakewa
Don haka Tabbas Dole Ka Yabawa Kabilar Hausa wajen wannan Tsari Nata.
Alhamdulillah Wassalatu Wassalamu Ala Rasulullahi
Muhadu Afitowa Ta Gaba.
Amb. Rufai Bunyamin MakwararDarul Qadereeya Jos